Jump to content

Aljannah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
ImageAljannah
Garden of Eden (en) Fassara
Image
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na mythical location (en) Fassara da otherworld (en) Fassara
Hannun riga da wuta

Aljannah; Wani ni'imtaccen muhalli ne da Allah yayi tanadinsa ga bayinsa (mutane da aljanu) wadanda sukai biyayya a gareshi, a cikin wannan rayuwar ta duniya. Sannan ana haduwa da wannan ni'imtaccen muhallin ne a bayan wannan rayuwa ta duniya ta Kare, wato za'a fara haduwa da wannan ni'imar ta Aljannah ne tun daga farkon rayuwar kabari har ya zuwa lokacin da za ai ma kola hisabi (Tashin Alkiyama).

Aljannah cike take da lambuna da koramai da idanuwan ruwa masu dadi wacce bamai zartsiba, akwai farantai na zinare da lu'ulu'u da kuma gadaje na ni'ima da tufafi na alhariri koraye.

Aljannah tana da hawa hawa kololuwarta ita ce Jannatul Firdausi. Allah madaukakin sarki yace lallai masu takawa suna acikin gidajen aljannah mai idanuwan ruwa (46) kushigeta da aminci, kuna amintattu(47) kuma muka debe abinda ke cikin zukantansu na kyashi, (suna masu zama) 'yan uwan juna, suna kishin gida cikin fuskantar juna akan gadaje (48).