Gyaɗa a tushen tatugaggiyar gyaɗa bayan an gino ta kafin a tsigeta daga tushen taƙuli-ƙuli na gyaɗa da kantuPeanut collectionFayil:Gyaɗa me gishiri.jpghaka Gyaɗa yake in'an soyaGyaɗa me ɓawoDaffafan gyada
Gyaɗa (peanut) wani abinci[1] ne, asalinsa tsiro ne da ake shukawa, yana kuma fitar da ƴaƴa a cikin kasa ƙarƙashin jijiyoyinta. Kuma ana sarrafa shi ne don amfani da shi a matsayin abinci da sauransu ta hanyoyi daban-daban kamar wurin yin kunu[2], mai.[3][4] (mangyada), Madara[5], kuli kuli, ko zubawa a miyar taushe, da sauransu. Ana iya dafa gyada[6] ana iya soya ta, ana kuma yin kantu. Gyada[7] na da sinadarin dake gina jiki, "protein" wanda ke da amfani sosai a jiki, musamman ma wajen ƙara girman jiki da bai wa jiki kariya, shi yasa yake da kyau a riƙa amfani da shi a cikin abinci. Kuma ita gyada ta kasu Kashi daban daban, akwai, Kampala, yar dakar, Mai bargo da sauransu.[4]
Yawancin inda suke noma ta. Zamfara da Nasarawa da Kaduna da kuma Kwara. Duk dadai yanzu akwai sabon irin gyada da yake yi a jihohin yankin gabashin ƙasar nan, musamman ma jihohin Enugu da Anambra.[8]
Ana Sarrafa gyada ta hanyoyi daban-daban kuma ana amfani da ita a duk fadin duniya, sai dai a nan za mu duba kadan ne daga irin hanyoyin da ake sarrafa gyada a matsayin abinci.
Madaran Gyada, za a iya yin madara da gyada, idan aka sami danyen gyada sai a bare ta, a wanke sannan kuma a bari ta jiku a ruwa, sai a niketa, idan aka nika sai a tace, bayan an tace sai a dafa, idan ya dahu sai a bar ta ta huce, shikenan an samu madarar gyada, za a iya bai wa yara wadanda ba su samun cikakken abinci domin karin lafiya.
Mangyada, za a iya hada mai da gyada idan aka samu gyada aka bare ta, aka bar ta ta bushe, ko kuma aka samu wanda aka riga aka busar, sai a soya ta ba da wuta sosai ba ko kuma za a iya kin soyawa, soyawa ba dole ba ne, idan an soya, sai a nika ta, to, ta zama tunkuza bayan an nika, daga nan sai a matse tunkuzar ta hanyar juyawa, za'a ga mai din na kadan kadan daga jikin tunkuzar.
ana sarrafa gyada a samar da man kuli kuliKulikuli idan anason yinsa za'a bi yanayin da aka bi dan yin mangyda ne, amma a dai-dai lokacin da aka gama fitar da mai din gyadar daga jikin tunkuzar, to tunkuzar da aka riga aka fidda mai acikin ta, shine za'a haɗa da sinadirai kamar magi, gishiri, barkono, citta da kuma sikari da sauransu sai a rinka diba ana curawa ana soyawa da mai din da aka fitar, idan aka soya yasoyu, to ansama kulikuli.
A farkon shekarun 1970 lokacin da ake noma sosai a Najeriya, jahar Kano tayi suna wajen noman gyada wadda ake fitarwa kasashen waje, domin samawa kasar kudaden shiga. A wancan lokacin 'yan kasuwa kan tara buhunan gyadar da suka sayo daga kauyukan jahar a wani katon wajen kafin a kwashe su zuwa Lagas, inda ake fitar da su ta jiragen ruwa, da hakane kuma aka rika gina dalar gyadar a Kano. Sai dai kuma sannu a hankali wannan dalar gyadar ta bace bayan da aka mai da hankali wajen hakar man fetur da ke matukar kasuwa a kasuwannin duniya. To ko mai ya sa dalar gyada a jahar Kano tai batan dabo? Wani babban dalilin da gwamnati da jama'a ke ganin ya kai ga hakan shine na kwarewar da jama'a sukai wajen sarrafa gyadar, sabanin a baya inda babu injina da sauransu. Yayin da wasu kuma ke dora alhakin bacewar dalar gyadar kan man petur, wasu kuma na cewa mutuwar jiragen kasa a Najeriya ne ya hana safarar gyadar daga arewa zuwa Legas.